Sanata Dino Melaye

Yunukurin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye daga majalisardattawa, a matsayin dan majalisa mai wakiltar Kogi ta Yamma a ranar Asabar ya gamu da cikas,inda al’umma suka ki fitowa domin tantance su, a shirshiryen da hukumar zaben take yi na dawo da dan majalisar gida.

Sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta bayar, bayan kammala atisayen yiwa Dino Melaye kiranye daga wakilci a majalisar dattawa, mutane 18,742 kacal aka iya tantancewa a cikin mutane 189,870 da aka ce sun sanya hannu a takardun yiwa Sanatan kiranye.

LEAVE A REPLY