Tsohon Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da jam’iyyarsa ta PDP aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban  ƙasa a zaben 2019 mai zuwa.

Mai magana da yawun tsohon Gwamnan Sule Yau Sule ne ya tabbatarwa da DAILY NIGERIAN HAUSA cewar, Malam Ibrahim Shekarau ya rubutawa Jam’iyyar ta PDP wasiƙa yake sanar da ita aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben da ke tafe.

Malam Shekarau bayan ya yi shawara tare da tuntubar dukkan bangarorin al’umma, sannan ya yanke shawarar tsayawa wannan takara ne. A cewar Sule Yau Sule, ya kara da cewar nan gaba, kuma Sheakarau din zai yi gangamin bayyana takarar tasa a bainar jama’a.

idan ba’a manta ba, a ‘yan kwanakin da suka gabata ne tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, shima ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019 dake tafe.

Ya zuwa yanzu dai akwai mutum uku da suka bayyanar da aniyarsu ta tsayawa takarar Shugaban  ƙasa a PDP wanda suka hada da, Gwamnan jihar EKiti Ayodele Fayose da Sule Lamido da kuma Malam Ibrahim Shekarau.

 

LEAVE A REPLY