Alhaji Lai Mohammed

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta gabas, Sanata Ben Murray-Bruce ya zargi ministan yada labarai na tarayyar Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed da yin zuki-ta-malle bisa wata magana da ya yi a baya-bayan nan na cewa wai jam’iyyar APC za ta lashe zaben 2019 ba tare da fuskantar barazana ba domin kuwa ta cika alkawarin da ta daukarwa al’ummar kasar nan a lokacin yakin neman zaben 2019.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai aka jiyo Lai Mohammed din na cewa, “Gwamnatin na da yakinin sake dawowa a shekarar 2019 sakamakon cika alkawurran kamfe da muka yi musamman ta bangaren ayyukan raya kasa da kuma samar dawalwala ga mutanen kasa.

“Hanya mafi sauki da za samu kuri’ar mutane ita ce ta cika musu alkawurrukan da ka dauka a lokacin yakin neman zabe tare da yin ayyukan zai shafi rayuwarsu kai tsaye.”

Sai dai wannan batu na Lai Mohammed bai yi wa wasu jiga-jigai a jam’iyyar APC dadi ba musamman ma dai Sanata Ben Murray-Bruce da Reno Omokri.

Ben Bruce ya wallafa a shafinsa na twitter kalamai da suka kalubalanci wancan ikirari na Lai Mohammed, inda daga bisani kuma ya gargadi Lai Mohammed da ya daina sharara karya musamman a wannan lokaci na ibadun azumin watan Ramadana.

Shi ma Reno Omokri, wanda tsohon hadimi ne ga shugaba Goodluck Jonathan ya shawarci Lai Mohammed da ya daina shararawa ‘yan Nijeriya karya.

“Shin wani zai iya tunawa Lai Mohammed cewa azumi ba wai kawai kame baki daga ci da sha bane har da kame baki daga fadin karya! Lai, ka ji tsoron Allah!!!,” inji Omokri.

LEAVE A REPLY