A ranar litinin aka koma kotu domin cigaba da Shari’ar da ake yiwa Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta. Inda bayan zaman kotun masu bayar da shaida kan Shari’ar da ake yiwa Maryam Sanda suka ki bayyana gaban mai Shariah Yusuf Halilu na babbar kotun Abuja dake Jabi.

Mutanan da suka je domin bayar da shaida akan Matyam sun hada da mahaifiyarta Maimuna Aliyu da dan uwanta Aliyu Sanda da kuma mai yi mata aiki a gida Sadiya Aminu.

Ana dai zargin wadannan mutum ukun da kare rashin gaskiyar da Maryam ta yi na halaka mijinta da kanta, Bilyaminu Bello, da ga tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Bello Halliru a ranar 19 ga watan Nuwamban 2017.

Mai Shari’ah Yusuf Halilu ya dage karar zuwa 19 ga watan Afrilu domin cigaba da sauraren karar, kamar yadda lauyan wanda ake kara Mista James Idachaba ya nema.

Mista Idachaba ya shaidawa kotu cewar, shaidun da yake da su, wadan da zai gabatarwa da kotu sun yi layar zana a harabar kotun, dan haka ya nemi a dage karar zuwa lokaci na gaba.

Lauyan ya nemi kada kotu ta yadda da batun Lauyan wanda ake karewa Joseph Daudu inda ya nemi kotu da ta yi watsi da shari’ar tun da shaidun da za’a gabatar sun yi layar zana a zaman kotun.

“Muna matukar adawa da duk wani yunkuri na korar  wannan Shari’ah da ake yiwa Maryam Sanda, mun gabatar da takarda mai shafi 22 na shaidun da muke da su kan wannan Shari’ah, dan haka babu muhallin korar wannan Shari’ah”

Tunfarko dai, Lauyan da yake kare Maryam Sanda, Joseph Daudu ya nemi kotu ta yi watsi da wannan Shari’ah a cewarsa, lauyan da yake kalubalantar Maryam Sanda bai bi hanyoyin da suka dace ba wajen shigar da ainihin karar.

Abinda lauyan da yake kalubalantar Maryam Sanda yace sam ba zata sabu ba, a cewarsa sun shigar da kara bisa doka, kuma sun tanadi dukkan shaidun akan wannan Shari’ah.

A cewar Daudu, wannan Shariah kama yayi tun farko a tura ta zuwa ofoshin antoni janar na kasa tun lokacin da ‘yan sanda suka kammala bincike.

Yace, ‘yan sanda ba su da hurumin gabatar  da wanda ake zargi da laifin kisan kai a gaban kotu, Antoni janar shi ne kadai yake da hurumin gabatar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Mista Daudu ya roki kotu da ta gaggauta korar wannan Shari’ah, domin ‘yan sanda sun gaza yin abinda doka tace kanirin wannan Shari’ah.

NAN

LEAVE A REPLY