Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana ficewa daga cikin jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’i Mai mulki ta APC.

Sauya shekar ta Shekarau ta biyo bayan rashin adalcin da akai masa shi da magoya bayansa da uwar jam’iyyar ta Kasa ta yi masa shi da magoya bayansa a cikin jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito cewar anyi wata ganawa a jiya da daddare tsakanin Tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a babban birnin tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY