Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya zargi Shugaban jam’iyyar na kasa John Odigie-Oyegun da yiwa shirinsa na sasanta rikicin cikin gida da ya dabaibaye ‘ya ‘yan jam’iyyar kafar ungulu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tun farkon wannan shekarar ya amince da nadin Tinubu a matsayin wanda zai sasanta rikicin da ya dabaibaye ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a fadin tarayyar kasarnan, wannan aiki ne da shi Tinubun ya fara tun farkon watan da ya gabata, yana kokarin zantawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Haka kuma, a wata wasika mai shafi takwas da Tinubu ya rubuta a ranar 21 ga watan fabrairu wadda aka aikewa da Shugaban kasa da mataimakinsa da kuma Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar dokoki na kasa kwafin wasikar, Tinubu ya zargi Mista Oyegun da yiwa shirin na Tinubu kafar ungulu.

Ya zargi Shugaban jam’iyyar na kasa da rashin bashi hadin kai, yace ba abinda Oyegun yake yi illa kokarin sabauta kokarinsa na ganin an gyara lamuran da suka tabarbare a cikin jam’iyyar.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, yace ya fara wannan aikin da budaddiyar zuciya, ya nuna matukar kaduwa kan yadda shi Oyegun yake ta kokarin ganin ya sabauta wannan aikin da yake yi wanda zai taimaki jam’iyyar domin magance rikice rikicen da suka yi mata daurin butar malam.

Yace “Daga fara aikin nan nawa, na shaidawa Shugaban kasa cewar zan yi aiki tsakani da Allah domin ganin nayi abinda ya dace da aka bani nayi”

“Abin da na fara yi tun bayan doramin wannan aiki, shi ne gabatar da kaina ga uwar jam’iyyar APC domin na shaida musu aikin da Shugaban kasa ya dora min a wuyana domin sasanta ‘ya ‘yan jam’iyyarmu da basa ga miciji da juna”

“A lokacin da na ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC domin gabatar da aikin da aka dora min, a mataki na kasa da jihohi da kuma kananan hukumomi”

“A matsayinsa na Shugaban jam’iyya, yayi alkawarin bani cikakken hadin kai da goyon baya kan wannan aiki da aka dora min, sannan kuma yayi alkawarin bani dukkan wasu bayanai da zasu taimaka min cin nasarar wannan aikin domin samun nasara tsakaninmu da kuma bangaren jihohi na jam’iyya”

“Abin takaici, hadin kai da goyon bayan da akai min alkawari domin ciyar da wannan jam’iyya da duk muka yi imani da ita ya zama fankam fayo a wannan tattaunawa da muka yi. Ina tabbatarwa da duk wanda yake da burin samun nasarar wannan jam’iyya tamu ya sani cewar, ba zan taba yarda abubuwa su tabarbarewa karkashin kulawa ta ba”

Sai dai kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto Oyegun bai samu ba domin mayar da martani kan wannan zargi da jagoran jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu yayi masa.

LEAVE A REPLY