Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar III

Hassan Y.A.Malik

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a jiya Laraba ya bayyana cewa, har yanzu akwai tsananin cin hanci da rashawa da ya ke faruwa a cikin gwamnatin Nijeriya, inda ya koka da cewa babu yadda za a yi kasar Nijeriya ta ci gaba a wannan yanayi da ta ke ciki.

Sarkin Muslimin, wanda shi ne shugaban majalisar al’amuran addinin musulunci na kasa, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gaggauta tsamo fulani makiyayan da ke aikata kashe-kashen al’umma, domin wadancan nau’in fulani un haddasa rashin yadda tsakanin manoma, sauran al’umma da fulani makiyaya na gaskiya.

Sarkin musulmi ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen taron kaddamar da wani littafi da aka wallafa don karrama shugaban hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a, JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, inda Sarkin musulmin ne ya zauna a matsayin uban taro.

Ya ci gaba da kokawa kan yadda a halin yanzu kasar Nijeriya ta rasa mutanen da za a iya kira da iyayen kasa, a maimakon haka, sai kasar ta zama ita ce uwar kowa. A yau a Nijeriya, bama karrama mutanen kirki sai wadanda suka aikata abin tsiya, abin ki. Ana iya gane mutanen kirki ne a kasar nan kawai bayan sun mutu, sai ka ga gwamnati ta sauya sunan wata jami’a ko filin tashi da saukar jiragen sama zuwa sunayensu.

“Ku duba batun wai maciji ya hadiye Naira miliyan 36. Wannan abin kunya ne, abin takaici. Shin ina mutuntaka da da’armu? A gaskiya ya kamata mu farka daga barcin da mu ke yi. Abubuwa sun tabarbare a kasar nan. Cin hanci da rashawa ya kai matuka a tsakakkaninmu. Dole mu tashi don ganin kawo karshensa.”

“Ba zai yiwu mu ci gaba da zama haka kawai kuma mu dauka abubuwa za su daidaita ba. Abubuwa sun baci matuka gaya. Dole mu nemi hanyoyin kyautata abubuwa,” inji Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III

Ya ci gaba da kokawa kan yadda wasu ke alakanta fulani jimlatan a matsayin masu kashe-kashe, inda ya bayyana cewa ya kamata tunaninmu ya shige na alakanta wata kabila da wani nau’i na mugun laifi.

LEAVE A REPLY