Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II

Daga Hassan Y.A. Malik

Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya ja hankalin shugabannin arewa da su kirkiro hanyoyin da za su kyautata rayuwar talakawansu ta yadda za su iya dogaro da kawunansu.

Sarkin ya yi wannan jawabi ne a wajen taron lakcar gabanin bikin yaye dalibai na jami’ar jihar da aka gabatar yau Asabar.

A jawabin nasa, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce, abubuwa biyu kacal jagororin arewa ya kamata su magance don cire yankin daga halin koma baya da ya ke ciki. Abubuwan kuwa sun hada da: Talauci da kuma Jahilci.

Bayan da Sarki Sanusi ya bayyana alkaluman da majalisar dinkin duniya da na hukumar kididdiga ta kasa suka fitar kan koma bayan ilimi a yankin arewa, musamman ma yanki arewa maso gabas da arewa maso yamma, inda nan ke da mafi yawan mutane a kasar Nijeriya, Sarkin ya ci gaba da cewa, wannan yanki shi ne ke da mafi girman adadin matan da ke mutuwa a yayin haihuwa, mafi yawan mutuwar kananan yara, rashin ilimi, da kuma rashin aikin yi.

Sarki Sanusi ya koka da cewa, wannan ko shakka babu shi ne ya yi haifarwa da yankin rashin ci gaban da ya kamata a ce ya samu duk kuwa da fadin kasa, da yawan mutane, da albarkar kasar noma, da kuma sauran ma’adanai da yanki ke alfahari da su.

Sarki Sanusi ya koka da yadda Almajirci ya zama ruwan dare a arewa, abinda Sarkin ya kira rashin kare martabar da kimar akidun musulunci ne ya haddasa hauhawar Almajirai a garuruwan arewa, domin kuwa kasashen musulmi a fadin duniya basa yadda wani iayali ya haifi adadin ‘ya’yan da ba za su iya bawa kyakkyawar kulawa ba.

LEAVE A REPLY