Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Jagoran PDP na kasa

Babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na kasa da aka yi jiya a shalkwatar sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayya Abuja, ya amince da nadin Shugaban majalisar dattawa na kasa Bukola Saraki a matsayin sabon jagoran jam’iyyar PDP na kasa baki daya.

A baya dai mataimakin SHugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu ne ke rike da wannan mukamin kasancewarsa, shi ne ke rike da babban mukami a cikin jam’iyyar, yanzu kuma bayan shigowar Bukola Saraki daga jam’iyyar APC zuwa PDP ya sanya jam’iyyar ta maye jagoran jam’iyyar da Bukola Saraki.

Haka kuma, wata majiya ta ruwaito cewar, magoya bayan Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki sun yi gangami jiya a Ilorin babban birnin jihar Kwara domin nuna gamsuwa da sauya shekar da Bukola Sarakin yayi zuwa jam’iyyar PDP.

 

LEAVE A REPLY