Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya sulale ya shiga zauren majalisar dattawa duk kuwa da tare masa hanya da jami’an tsaro suka yi a kofar gidansa na hana shi bin hanyoyin da zasu sadar da shi da zauren majalisar.

Bayan shigarsa zauren majalisar, Bukola Saraki ya sanya anyi adduar budewa da adduah kamar yadda aka saba, daga bisani kuma aka shiga tattauna batutuwan da suka shafi majalisar da kuma Shugaban majalisar.

Sufeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim K. Idris a ranar Litinin ya gayyaci Shugaban majalisar Bukola Saraki domiin ya bayyana a gaban rundunar ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja domin amsa tuhumar da ake masa kan batun fashin da aka yi a Offa jiharKwara.

A wasikar da aka rubuta a ranar 23 ga wannan watan nan, Sufeton ‘yan sandda na kasa ya aikewa da Shugaban majalisar Bukola Saraki da ya bayyana a gaban rundunar ‘yan sandan da misalin karfe 8 na safiyar yau Talata.

Sai dai kuma, da sanyin safiyar yau ‘yan sanda suka tarewa Shugaban Abubakar Bukola Saraki hanya domin hana shi zuwa zamanmajalisar na yau.

LEAVE A REPLY