Mataimakin Shugaban Kasa yemi Osibanjo sai Abba Kyari da kuma Winifred Ayo-Ita

Rohotanni daga fadar Gwamnatin Najeriya aranar Larabar nan sun nun cewar an samu mummunan sabani tsakanin Shugabar ma’aikatan Gwamnatin tarayya Winifred Oyo-Ita da kuma shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa Abba Kyari kan zargin badakalar Abdulrasheed Maina, ‘yan mintoci kadan kafin fara zaman majalisar zartarwa.

Wannan sanya zare baya rasa nasaba, da zargin da ita shugabar ma’aikatan ta yiwa Shugaban kasa kan batun dawo da Abdulrasheed Maina bakin aikinsa.

Majiya mai tushe ta tabbatarwa DAILY NIGERIAN HAUSA cewar, an jiyo ita shugabar ma’aikatan tana yin magana da karfi a gaban Abba Kyari cewar, ita fa ta kai makura a aikin Gwamnati,  dan haka ba zata lamunci shiga hanci da kudundune da ake yi mata.

Daga nan kuma, anganta ta isa wajen kujearar da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo yake zaune, tana yi masa korafi akan abinda Abba Kyari yake yi mata.

Daga baya kuma, anga Mai baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Munguno ya shiga cikin tattaunawar, daga nan kuma an hango sabon sakataren Gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha yana kokarin baiwa ita shugabar ma’aikatan hakuri yana rarrashinta.

Koma ya ake ciki zaku ji cikakken bayani zuwa anjima.

 

LEAVE A REPLY