Zauren MajalisarDattawa

Yau wata dambarwa ta faru a majalisar Dattawa. Wani Sanatan PDP daga jihar Ebonyi, Sonni Ogbuoji a ranar Laraba yayi nufin canza sheka daga PDP zuwa APC amma ‘yan uwansa Sanatocin PDP suka ci nasarar hana shi.

Mista Ogbuoji, ya nuna alamun zai sauya sheka daga PDP zuwa APC a lokacin da ya mike yana jawabi a gaban babban zauren majalisar Dattawa. Sanatan ya mike yana bayyana irin matsalolin da PDP take fama da shi a jiharsa, a sabida haka ya bayyana wannan a matsayin dalilin da zai sanya ya sauya shekar.

A lokacin da yake ta jawabin da yake nuna cewar ya bar PDP zuwa APC, ‘yan uwansa Sanatocin PDP sun muke tsaye inda suka tunkaro inda yake tsaye yana jawabi, inda suka hana shi cigaba da magana.

A daidai lokacin da Sanatocin PDP suka mike, sai yace “Na riga na gama yanke shawarar barin tsohuwar jam’iyyata a matakin jiha da tarayya” Fadin haka ke da wuya sai Sanatocin suka zo suna yin kuskus da shi.

Bayan kamar mintuna goma sha biyar suna yin kuskus tsakaninsa da Sanatocin PDP. An barke da sowwa a majalisar, an yi shiru a majalisar a lokacin da Sanatan ya kuma mikewa zai yi jawab.

Sanatan ya bayyana cewar, “Ina nan a cikin jam’iyyata ta PDP babu inda zani” Ma’anaSanatocin sunci nasarar shawo kan abokin aikin nasu inda ya fasa aniyarsa ta sauya sheka daga PDP zuwa APC.

“A lokacin da na mike domin sauya sheka, abokaina ‘yan PDP sun ci nasarar shawo kaina, kuma sakamakon yadda suka nuna min kauna da soyayya, ya sa na sauya tunanin sauya shekar da na kuduri aniyar yi tun da farko” A cewar Sanatan.

A lokacin da yake maida jawabi, Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, yace “Zan kasance a majalisar Dattawa a duk tsawon ranar yau, idan har ya sake canza shawarar dawowa APC”

LEAVE A REPLY