Marigayi Sanata Ali Wakili

Sanata mai wakiltar jihar Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, Ali Wakil ya rasu yana da shekaru 58 a duniya.

Makusancin ga Sanatan ya shaidawa DAILY NIGERIAN cewar Sanata AliWakili ya yanke jiki ya fadi ne a gidansa dake unguwar Gwarinpa a birnin tarayya Abuja a ranar Asabar da safe.

An garzaya da Sanatan zuwa asibitin Viewpoint dake Abuja,inda anan ne likitoci suka tabbatar da cewar yarasu. Ali Wakili yana da Sarautar Fagacin Bauchi a masarautar Bauchi.

Kafin ruwarsa, shi ne Shugaban kwamitin kula da batun talauci da yadda za’a rage radadinsa a majalisar dattawa, yana kuma daya daga cikin mutanan da ake jin amonmuryarsu a majalisardattawa.

 

LEAVE A REPLY