Hajjin shekarar 2018

Akalla a bana sama da Alhazai miliyan biyu  ne da suka fito daga kasashen duniya daban daban suka yi hawan Arfa a kasar Saudiyya yayin gudanar da ibadar aikin hajjin bana na shekarar nan.

Alhazan sun iso filin Arfa ne bayan da suka kwana a Minna,inda daga nan zasu fi hawan Arfa tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana. Hawan Arfa dai shi ne babban rukuni a cikin aikin hajji, domin duk wanda bai samu arfa ba har rana ta fadi ance ba shida aikin hajji.

Aikin hajji daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kamar yadda Allah ya aiko Manzonsa Sallallahu Alaihi Wasallam da sakon Musulunci.

Bayan Musulmi sun kammala hawan arfa, zasu yi jifan shedan su yi aski kuma su yi dawafi. Abinda yake nuna cikar aikin hajjinsu.

Daga Najeriya dai kasa da Alhazai dubu dari ne ska samu zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali.

Hukumomin kula da aikin hajji a Najeriya sun bayyana cewar an samu raguwa matuka ta masu zuwa Hajji a bana, duk kuwa da sun ce an rage kudin aikin hajjin ba kamar na bara ba, amma dai mutane basu samu ikon biyan zuwa hajjin ba.

Wannan kuma mutane na ganin yana da alaka da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi ne a Najeriya.

LEAVE A REPLY