Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Sakatren Gwamnatin tarayya Boss Musstapha ya kaddamarda website na ofishinsa da aka inganta na Naira miliyan 64 a babban birnin tarayya Abuja, wanda za’a iya kamawa a www.osgf.gov.ng don ganin ayyukan ofishin Sakataren Gwamnatin.

Sakataren ya bayyana a ofishinsa cewar ba an kashe Naira miliyan 64 ne kawai domin gina website dinba, a cewarsa, an sayi kwamfutar Laptop sannan kuma an baiwa ma’aikatan ofishin nasa horo akan website din.

Sai dai kuma Sakataren Gwamnatin bai bayyana ko na’urar kwamfuta nawa aka saya ba, bai kuma yi karin bayani ba akan nawa aka kashe wajen horas da ma’aikatan ofishin nasa.

bayan haka, a shekarar 2017, an kashe naira miliyan 64 domin website din da kuma sayan Laptop domin amfanin ma’aikatan ofishin sakataren gwamnatin tarayyar.

Boss Mustapha ya yi kaarin bayanin cewar, za’a dinga bayyana manufofin Gwamnatin Buhari a wannan wwebsite da kuma duk abubuwan da suka shafi Gwamnatin tarayya da abubuwan da take aiwatarwa.

 

 

LEAVE A REPLY