Shugaban kasa Muhammadu Buhari

A saƙonsa da ya aikewa da ‘yan Najeriya ta kafar akwatintalabijin ranar litinin da safe, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yiwa al’ummar ƙasa fatan alheri, da kuma taya su murna shiga sabuwar Shekarar 2018 lafiya.

A cikin jawaban da ya gabatar, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama, ciki kuwa har da batun karancin man fetur da dangoginsa da ake fama da shi a duk fadin Najeriya, a batun tsaro da wutar lantarki da tattalin arziki da kuma batun nan da aka jima ana cecekure, na sake fasalta Najeriya.

“Sako na a gareku a wannan safiya ba wai kawai ya ta’allaka ga taya juna murnar shiga sabuwar Shekara bane, dole ne na sanar muku cewar, wannan gwamnati tamu ta himmatu wajen cika dukkan alkawuran da muka daukarwa ‘yan Najeriya na samar da canji abin misali”

“Wannan Gwamnati ta APC ta himmatu matuka kan batun giggina hanyoyi a ko ina a sassan Najeriya, matsalar rashin kyawun hanyoyi na daya daga abinda ya damu Gwamnati, dan haka muke shiri babu dare babu rana wajen ganin mun inganta manya da kananan hanyoyi a Najeriya”

“Ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma makamashi daya ce daga cikin jagororin tafiyar da wannan Gwamnati, kuma ta himmatu wajen biyan bukatun ‘yan Najeriya musamman wajen ganin mun inganta tsarin da ake tafiya akansa na yin manyan ayyuka ya dace da zamani kuma mu tafi kafada da kafada da sauran kasashen duniya ta fuskar ayyukan raya kasa”

Haka kuma, Shugaban yayi bayanin yadda Gwamnatin take aiki dare da rana akan batun sufuri ta hanyar jirgin kasa, Shugaban yace, Gwamnati na yin kokari musammana wajen ganin ta samar da ingantacce layin dogo da ya tashi daga Legas zuwa Kano, da kuma sauran sassan najeriya domin buknkasar harkar tattalin arziki.

Da kuma ya juya kan bangaren giggina hanyoyi, Shugaba Buhari ya sha alwashin magance matsalar hanyoyi da ‘yan Najeriya suke fama da ita. “Manyan hanyoyi guda 25, zasu sha garambawul ta hanyar sanya kudi naira biliyan 100 daga tsarin nan na SUKUK, wanda ko wanne sashi na kasarnan zai amfana da wannan tsari”

“Gwamnatinmu zata cigaba da aikin tagwaita hanyoyin Kano-Maiduguri, Abuja-Lakwaja-Benin, Suleja-Minna, Oyo-Ogomasho, Enugu-Fatakwal, Onisha-Enugu, duk suna daga cikin hanyoyin da Gwamnati zata himmatu wajen gannin an kammala aikin Tagwaitasu zuwa masu hannu biyu”

“Haka kuma, Gwamnati ta amince a sake gina hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano, wadda take cikin mawuyacin hali, nan ba da jimawa ba za’a fara wannan aiki, kuma muna sa ran kammala shi nan da shekarar 2019”

Da ya juya bangaren samar da hasken wutar lantaki kuma, Shugaba Buhari yace, a ‘yan kwanakin nan ‘yan Najeriya shaida ne wajen yadda ake samun karuwar hasken wutar lantarki a kusan dukkan sassan kasarnan, wannan kuma ba komai ba, sai irin yadda Gwamnati ta himmatu wajen ganin an samarwa da ‘yan Najeriya ingantacciyar wutar lantarki. A cewar Shugaban kasa.

A bagnagren noma kuwa, Shugaba Buhari ya yabawa ‘yan Najeriya da suka mayar da hankali kan bangaren noma, “A farkon zuwa na wannan Gwamnati, nayi kira ga ‘yan Najeriya da su koma noma, kuma noman da ‘yan Najeriya suka komai sai am-barka, domin ina mai cike da farin cikin yadda mutane suka mayar da hankalin kan batun noma, haka kuma, nan ba da jimawa ba zamu haramta shigo da Shinkafa Najeriya, domin baiwa manoman shinkafa na gida damar noma wadda zamu bukata”

Shugaba Buhari ya karkare jawabin nasa da godiya ta musamman ga ‘yan Najeriya musamman yadda suka dukufa wajen yi masa adduah a lokacin da ya kwanta rashin lafiya a shekarar da ta gabata, yace kuma Alhamdulllah ya samu sauki kamar bai taba jinya ba.

Daga karshe ya yiwa ‘yan Najeriya Barka da shiga sabuwar Shekarar milidiyya ta 2018.

 

LEAVE A REPLY