Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewar ta kashe a kalla mayakan kungiyar Boko Haram guda bakwai tare da kwato wasu makamai daga garesu, a kauyen Azaya Kalmari dake yankin karamar hukumar Mafa a jihar Boorno a ranar  Juma’a.

Onyema Nwachukwu mataimakin darakntan yada labarai na rundunar ‘Lafiya Dole’ shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Maiduguri.

Ya cigaba da cewar, ‘yan ta’addar da misalin karfe 12 na rana, a daidai lokacin da rundunar sojojin take wani aikin binciken kwakwaf a wasu kauyukan karamar hukumar Mafa, suka barko musu.

“Amma cikin taimakon Allah jami’anmu dake bakin aiki suka mayar  da wuta, kuma har suka karya lagon ‘yan kungiiyar ta Boko Haram, inda suka kashe mutum bakwai daga cikinsu, sannan suka ci nasarar kwace bindigogi samfurin AK47 da AK56 da kuma tarin Albarusai.”

“Rundunar sojojin ta kuma ci nasarar kakkabe dukkan wasu ‘yan ta’adda daga kauyukanModuhum da Njimtular da Hayaba da Gana da kuma Hayaba Kura da Hashime da Azaya Kura da kuma kauyen Azaya, dukkansu yankuna ne a cikinkaramar hukumar Mafa” A cewar Nwachukwu.

NAN

LEAVE A REPLY