Sufeton ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Kpotum Idris, ya bayar da umarni tura jami’an tsaro na ‘yan sanda guda dubu biyar 5000 tare da jirgi mai saukar ungulu da manya manyan motoci masu sulke a harabar wajen da za’a yi babban taron jam’iyyar APC mai mulki na kasa, da aka shirya yi a Asabar din nan 23 ga watan Yuni a filin Eagle Square dake babban birnin tarayya Abuja.

Wannan bayani ya fito ne daga Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa Jimoh Mashood a wata sanarwa da ya fitar, inda yake bayarda umarnin aiki da umarnin Sufeton ‘yan sanda na kasa, don yin taron jam’iyyar lami lafiya.

 

LEAVE A REPLY