Daga Yasir Ramadan Gwale

Rundanar soja shiyya ta daya tare da hadin guiwar hukumar tsaron farin kaya ta kasa, sun ci nasarar cafke wasu mutane biyu dake safarar makamai akan hanyar Funtua zuwa Gusau a Zamfara ranar lahadi.

Kakakin rundanar sojan Nigeria, Sani Usman ya bayyana hakan ga manema labarai ranar litinin. Binciken gaggawa ya nuna cewar mutanan na kan hanyarsu ne don hannanta wadnnan makami ga batagari.

Burgediya Janar Usman ya kara da cewa, an kama mutanen na tuka mota kirar “golf” mai dauke da lamba AWE-534-AA (lambar jihar Nassarawa) na dauke da albarusai kimanin 1479. Ya kara da cewar, mutanan biyu na tsare a hannun jami’an tsaron farin kaya.

Burgediya Usman ya ci gaba da cewa, an tura rundunar soja garin Dangulbi a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara domin fuskantar batagari, haka kuma, rundunar taci nasarar damke wasu batagari mutum uku a yayin da suke sintiri a garin.

“Runfunar taci nasarar kwato bunduga samfurin AK-47 da harsasai 40 da kuma albarusai kimanin 45,500, da wayar hannu samfurin Nokia da layin Airtel guda uku” inji kakakin rundunar sojan Nigeria.

A wani labarin mai kama da wannan kuma, kakakin ya bayyana cewar, rundunar sojan ta cafke wani mutum da ake zargi barawon shanu ne mai suna Abdullahi Nakogiwo a garin Dalingen a yankin karamar hukumar mulkin Rabah dake yankin Sokoto.

LEAVE A REPLY