Sakatariyar Jam'iyyar APC da Gwamna Malam Nasiru el-Rufai ya rushe

Sakatariyar jam’iyyar APC a jihar Kaduna bangaren su Sanata Hunkuyi ta gamu da fushin mai Rusau a safiyar yau talata, inda Gwamna Nasirsu el-Rufai da kansa ya hau mota ya turmushe ginin sakatariyar.

Shi dai wannan ginin sakatariyar APC da aka rushe mallakin Sanata Suleiman Hunkuyi ne, ya kuma bayyana abinda ya faru a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewar Gwamnan jihar @GovKaduna Mallam @elrufai da kansa ya tuka motar da ta markade ginin Sakatariyar.

Ginin wanda yake Lamba 11 titin Sambo, Gwamna yaje ya rushe shi tare da rakiyar jami’an tsaro masu yawan gaske. Wannan dai wani sabon fada ne wanda ba zai haifarwa da jam’iyyar APC da mai ido ba a jihar ta Kaduna.

Shi dai wannan ginin mallakar Sanata Suleiman Hunkuyi ne, wanda shi da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya suke jagorantar bangaren jam’iyyar APC wanda ya balle daga biyayya ga Gwamna Nasiru el-Rufai.

Idan ba’a manta ba a makon da ya gabata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon Gwamnan jihar Legas Sanata Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai jagoranci sasanta ‘yan jam’iyyar APC da ba sa ga miciji da juna.

Faruwar wannan al’amari a jihar Kaduna ya sanya shakku kan yuwuwar dinke barakar da take damun jam’iyyar APC a jihar ta Kaduna,domin jama’a da dama na tunanin da wuya a iya dinke wannan baraka ta su Sanata Hunkuyi da kuma Gwamna el-Rufai.

 

LEAVE A REPLY