Shugaba Muhammadu Buhari

Daga Hassan Abdulmalik

Adadin rayukan da suka salwanta a rikicin jihar Filato a yanzu ya haura 200, inda al’umma a wannan yanki da ke tsakiyar arewacin Nijeriya ke cikin tashin hankali da zaman ɗar-ɗar.

Kwamandan rundunar tsaro na Nijeriya, Janar Abayomi Gabriel Olanisakin ya umarci da a sake turawa da wasu dakaru na musamman jihar ta Filato don karfafawa wadanda aka tura tun da farko don ganin cewa an kawo karshen tashin hankali cikin gaggawa.

Tun a jiya Litinin ne rundunar ta musamman ta sauka a Jos, babban birnin jihar ta Filato, kuma da saukan ne shugaban rundunar aiki na Operation Safe Haven OPSH, Manjo Janar AM Atolagbe ya yi musu jawabi game da yanayin aikin da ke gabansu da kuma yadda za su tunkare shi.

A wata sanar da kakakin rundunar tsaro na kasa, Birgediya Janar John Agim, ya fitar ya ce, “Rundunar sojin Nijeriya na dada tabbatarwa da duk wani dan kasa na gari da ke a jihar Filato cewa yana cikin tsaro da kariyar soja.”

Sanarwar ta ci gaba da jan kunnen matasa ‘yan ta more da cewa, “Duk wani matasahi da ya bari wani ko wasu suka yi amfani da shi a matsayin dan daba, to, fa zai dandana kudarsa in ya shiga hannun hukuma.”

“Haka kuma muna kira ga makiyaya da manoma da su guji daukar doka a hannunsu; a maimakon haka, su gaggauta sanar da jami’an tsaro da zarar sun fuskaci barazana ko sun zargi wani ko wasu da haifar da barazana ga lafiya, dukiya da rayukansu.” A cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY