Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa, ta nemi dukkanin ‘ya ‘yan jam’iyyar dake mazabar dan majalisar dattawa ta Kogi ta yamma da su kauracewa duk wani yunkuri na yiwa Sanata Dino Melaye kiranye da a ke shirin gudanarwa a ranar Asabar 28 ga watan Afrilu.

A wata sanarwa da ta fitar a birnin Lakwaja ranar Juma’a, jam’iyyar ta bayyana cewar ko kadan bata goyon bayan batun yiwa dan majalisar dattawa Sanata Dino Melaye kiranye, wanda ake sa ran fara shirin yi masa kiranyen a gobe Asabar.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta sanya ranar Asabar 28 domin fara shirye shiryen yiwa Dino Melaye kiranye.

INEC tace za’a fara tantance sanya hannun wadan da suka nemi dawo da dan majalisar daga wakilcin da yake yi, daga bisalin karfe 8 na safe zuwa 2 na rana, a akwatuna 552 a kananan hukumomi bakwai dake mazabar dan majalisar dattawa ta Kogi ta Yamma.

Darakta tarawa da adana muhimman bayanai na jam’iyyar PDP, Dickson Achadu ya bayyana yunkurin yiwa Sanata Dino Melaye kiranye da cewar rikicin cikin gida ne dake neman cinye jam’iyyar APC.

Daga nan ya bukaci mambobin jam’iyyar PDP da su kaucewa dukkan wani yunkuri na yiwa dan majalisar dattawa Dino Melaye kiranye.

Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana dukkan goyon bayanta ga Sanata Dino Melaye,saboda irin gwagwarmayar da yake yiwa domin al’ummar kasarnan su samu kyautatatuwa da ingantacciyar rayuwa.

Daga nan kuma, jam’iyyar ta nemi INEC da jami’an tsaro da su tabbatar ba a yi amfani da su wajen danne hakkin Dino Melaye ba.

Sannan kuma, jam’iyyar PDP ta yi kira ga dukkan ‘ya ‘yanta da su zamo masu bindoka da tsari da kuma sallamawa dukkan abinda ya dace da samun zaman lafiyar wannan batu.

A nasu bangaren, rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kogi ta tabbatar da al’ummar dake mazabardan majalisar dattawa ta Kogi ta Yamma, tabbacin samun cikakken zaman lafiya yain gudanarda wannan atisayen.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Kogi, Ali Janga ya tabbatarwa da al’ummar yankin samun cikakken goyon bayan ‘yan sanda, tare da tabbatar musu cewar ba za’a bar ‘yan daba su ci karensu babu babbaka ba a wannan mazaba.

 

LEAVE A REPLY