Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a ranar Litinin din nan zai gana da kunshin ‘yan sabuwar PDP da suka balle suka kafa jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Kawu Baraje.

DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Sanata Kwankwaso dan mjalisar  dattawa mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar  dattawa, da sauran gaggan mutanan da suka balle suka kafa jam’iyyar APC duk zasu halarci tattaunawar.

Idan za’a iya tunawa a ranar Lahadin da ta gabata jagoran ‘yan sabuwar PDP Kawu Baraje a brnin Ilori, ya bayyana cewa zasu gana da mataimakin Shugaban kasa domin tattaunawa domin kawo karshen turka turkar da ake fama da ita tsakanin ‘yan sabuwar  PDP din da kuma bangaren ‘yan APC din.

Baraje ya bayyana cewar, yana fatan a karshen tattaunawar  da za’a yi tsakanin bangarorin biyu ta zama mai ma’ana kuma ta haifar da da mai ido, domin cigaban jam’iyyar ta APC.

A cewarsa, mutanan da yake jagoranta na sabuwar PDP zasu fito da matsayarsu ce bayan kammaluwar wannan taron.

“Bayan kammalaluwar wannan zaman ne ake sa ran zasu yi zama na musamman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin samun matsayarsu ta karshe”

 

LEAVE A REPLY