Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci  zaman majalisar zartarwa na wannan makon da ya guda a fadar Shugaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Najeriya zuwa London domin ya gana da likitocinsa,dominduba shi.

Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata Ministoci 18 ne kacal suka halarci zaman majalisar da Osinbajo ya jagoranta.

Daga cikin Ministocin da suka halarci zaman majalisar na wannan makon akwai: Lai Mohammed (yada labarai), Abdulrahman Danbazzau (harkokin cikin gida), Chris Ngige (kwadago), Adamu Adamu (Ilimi), Adebayo Shittu (Sadarwa), Usani Usani (Niger Delta affairs), Ogbonnaya Onu (Kimiyya da kere kere) and Rotimi Amaechi (Sufuri).

Sauran su ne Zainab Ahmed (kasafi da tsare tsare), Steven Ocheni (kwadago), Anthony Onwuka (Ilimi), and Heneiken Lokpobiri (Albarkatun noma).

Ragowar su ne Omole Daramola (niger Delta), Osagie Ehinare (Lafiya) Hadi Sirika (zirga zirgar jiragen sama), and Mustapha Baba Shauri (Makamashi).

LEAVE A REPLY