Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo tare Shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da Janar Tukur Burtai shugaban hafsan sojan kasa da Shugaban sojan sama AVM Sadiq Abubakar da mai baiwa Shugaban kasa shawara tafuskar tsaro Babagana Munguno da sifeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris.

Daga cikin Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da gwamnonin Kaduna Nasiru el-Rufai da na Jigawa Badaru Abubakar da na Katsina Bello Masari da na legas Akinwunmi Ambode da Gwamnan Ondo Rotimi Akerelodu da na Neja Abubakar Bello da Godwin Obaseki na jihar Edo.

Sauran Gwamnonin su ne David Umahi na Ebonyi da AbdulAziz Yari Abubakar na jihar Zamfara kuma Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, sai kuma Willi Obiano na jihar Anambra da Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom.

Sannan kuma akwai Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Gida Mustapha da kuma ministar kudin tarayyar Najeriya, Kemi Adeosun.

LEAVE A REPLY