Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya caccaki tsohon Shugaban kasa Chif Olushegun Obasanjo ina ya zarge shi da barnatar da biliyoyin daloli a banza a harkar wutar lantarki a Najeriya.

Buhari yace Obasanjo ya kashe fiye da dalar Amurka biliyan 15 domin samar da wutar lantaki, wadda yanzu halin da ake ciki babu kudin babu wutar lantarkin, kudin sun tafi a banza, yace dole Obasanjo ya amsa tambayoyi akan haka.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar Gwamnati dake Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin Shugabannin kungiyar ‘Buhari Support Organisation’ wata kungiyar magoya bayan Buhari karkashin jagorancin Shugaban hukumar kwastam ta kasa, kanar Hameed Ali mai ritaya.

Wannan kungiya ta BSO ita ce ke jagorantar sake neman zaben Shugaba Buhari karo na biyu a shekarar 2019.

Shugaba Buhari ya bayyana cewar an kashe wadannan makudan kudaden ne tsakanin shekarun 1999 zuwa shekarar 2014, abinda ya kunshi zamanin Mulkin marigayi Umar YarAdua da kuma tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

LEAVE A REPLY