Sanata Abdulaziz Nyako

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, Sanata Abdul’aziz Murtala Nyako ya bayyana cewa tuni tattaunawa ta yi nisa  tsakaninsa da Kwankwaso da wasu jiga-jigan siyasa kan batun sauya sheka daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa wata jam’iyyar.

Sanata Nyako, a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Premium Times ya bayyana cewa dab ya ke da ya jagoranci magoya bayansa da dimbin magoya bayan mahaifinsa kuma tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako su fice daga jam’iyyar APC sakamakon abin da ya kira rashin mutunta su da ba a yi a jam’iyyar.

Nyako ya bayyanawa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya kan batu ficewa daga APC.

“Bamu da wani zabi da ya wuce na  mu bar jam’iyyar APC, amma har yanzu bamu yanke hukunci kan jam’iyyar da za mu koma tare da dukkanin tsare-tsaren shugabncinmu ba. Na yi magana da Farfesa Jerry Gana kan batu shiga jam’iyyar SDP. Haka kuma na yi magana da Attahiru Bafarawa kan batun komawa jam’iyyar PDP da shi Bafarawan ne ke son mu dawo jam’iyyar.

“Tuni na shirya wani zama tsakanin mahaifina, Admiral Murtala Nyako (ritaya) da Bafarawa. A ranar Alhamis din da ta gabata ma sai da na yi takakkiya zuwa garin Abeokuta na gana da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo kan batun shiga jam’iyyar ADC, kuma ya tura ni wajen Oyinlola kuma tattaunawarmu ta tsaya akan za a bamu gurbi a jam’iyyar ADC na mu da magoya bayanmu da kuma tsarin shugabancinmu.

“Haka kuma na yi magana da Kwankwaso kafin a gudanar da zaben shugabanin jam’iyyar APC kuma ya tabbatar min da cewa sun kammala dukkan shirye-shirye na kafa wata sabuwar jam’iyya kuma har an bani kundin tsare-tsaren wannan sabuwar jam’iyyar ta su Kwankwaso tun wata guda da ya gabata.

“Jam’iyyar ta su Kwankwaso muna sa rai za ta samu rijistar hukumar zabe tare da wasu guda 4 nan bada dadewa ba. Ina matukar farin ciki za mu bar APC tun kafin lokaci ya kure,” inji Sanata Nyako.

LEAVE A REPLY