Ministan kula da zrga zirgar jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika ya kaddamarda sabon kamfanin zirga zirgar jiragen saman Najeriya da aka bayyana sunansa da ‘Nigeria Air’ domin fara harkar sufurin jiragen sama.

An yi bikin kaddamar da jirgin ne a ranar Laraba a dandalin bajekolin jiragen sama na Farnborough dake birnin Landan na kasar Burtaniya.

Bikin nuna sabon kamfanin jirgin, an yi shi ne a wata cibiyar hada hadar jiragen sama mafi kasaita da kuma kwararrun akan harkar jiragen sama.

 

LEAVE A REPLY