Shugaba Muhammadu Buhari

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito Ministan Sadarwa na Najeriya, Adebauo Shittu a ranar laraba, ya ziyarci fadar Shugaban kasa domin bayyana masa irin cigaban da ake samu wajen kammala shirye shiryen harba tauraron Ɗan-Adam na $550m daga kasar Chana.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar Shugaban kasa, Minista Adebayo Shittu, ya bayyana cewar, sun kammala duk wani shirye shirye da Bankin EXIM na kasar Chana domin cimma yarjejeniyar biyan kudin wannan tauraro da Najeriya zata harba sararin samaniya daga kasar Chana.

Ministan yace, a cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin EXIM da kuma Gwamnatin Najeriya shi ne, shi bankin EXIM zai biya kashi 85 na kudin, yayin da Gwamnatin Najeriya zata biya kashi 15 na adadin wannan kudin.

Ministan ya kara da cewar, Shugaban kasar ya gamsu da dukkan bayanan da yayi masa dan gane da tauraron dan-adam din, a ganawar da suka yi a kebe da Shugaba Buhari a fadar Gwamnati a  jiya laraba.

LEAVE A REPLY