Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Najeriya ta daga sama da akalla mataki biyar a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitarwa kowanne wata kan kasashen da suka fi iya kwallo a Duniya. Yanzu haka dai Najeriyar ita ce ta 47 a duniya kuma ta shida a Afrika da akalla maki 635.

A jadawalin da ya gabata kafin na yau, Najeriyar ita ke a matsayin ta 52 a jerin kasashen da suka fi iya kwallo da maki 609.

A nahiyar Afrika Tunisia ce a kololuwa kuma ta 14 a duniya sai kuma kasashen Senegal da Jamhuriyar Dimocradiyyar Congo da ke mara mata baya a matsayin na 28 da 38 a duniya.

A duniya baki daya kuma kasar Jamus ce ke ci gaba da rike kambunta a matsayin ta daya sai kuma Brazil ta biyu yayinda Belgium wadda a baya ke matsayin ta 5 yanzu ta dawo ta 3.

A ranar 17 ga watan Mayu mai zuwa ne Fifar zata kara fitar da wani jadawalin wanda hukumar take la’akari da yadda kasashe suke buga gasa da kuma yadda suke samun nasarori a wasan kwallon kafa.

LEAVE A REPLY