Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya a kwanakin baya

Wakilin Najeriya na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya, Mista Babatunde Nuruddeen, ya gabatar da wani kuduri gaban Majalisar Ɗinkin Duniya inda yake bukatar a kawo sauyi kan batun kwamitin tsaro na Majalisar ta dinkin duniya dake birnin Nuyok na kasar AMurka.

A cewar wakilin na Najeriya, Babatunde yace, wariyar da ake nunawa kasashe musamman nahiyar Afurka a kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya, yace sam ba daidai bane, a cewarsa ci gaba da tafiya yadda ake, akwai zalinci da kuma danniya ga kasashen Afurka.

Ya cigaba da cewar, a matsayin kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya na kwamitin koli, amma ce mambobi 15 ne kacal gareshi, yace wannan da sake, a cewarsa, dole in dai Adalci ake so a samu karin yawan wakilan wannan kwamiti.

Wannan kwamiti dai na tsaro, shi ne babban kwamiti kuma na koli a dukkan kwamitocin majalisar dinkin duniya. Domin, kwamitin shi ne yake da alhakin sanyawa wata kasa takunkumi, ko kuma sassauta mata takunkumi, ko ma yin amfani da karfin soja akan wata kasa da bukatar hakan ta tasowa majalisar dinkin duniya.

Najeriya dai ita ce, wakiliya kwaya daya daga yankin kasashen Afurka ta yamma a majalisar tsaron, wadda Babatunde Nuruddeen ke kasancewa a madadin Najeriya a ko da yaushe.

Shin ko wannan bukata da Najeriya ta gabatar zata samu karbuwa? Ku bamu ra’ayinku.

LEAVE A REPLY