Shugaba Muhammadu Buhari

Fadar Shugaban kasa ta musanta zargin da ake yi mata na goyon bayan maida ofishin jakadancin kasar Amurka daga babban birnin kasar Israeli Tel Aviv zuwa birnin Kudus mai tsarki, wanda yake da muhimmanci a wajen Musulmi.

Mai magana da yawun fadar Shugaban kasa, ya bayyana ‘yan jarida a Abuja cewar, tuni Gwamnatin Najeriya ta rubutawa kafar yada labarai ta Al-Jazeera da ta bayyana cewar Najeriya na daya daga cikin wadan da suka halarci bikin bude sabon ofishin jakadancin na Amurka, da su janye sunan Najeriya a cikin jerin sunayen da suka sanya.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyema ya nemi jakadan najeriya dake kasar Israeli da yayi bayanin dalilin kasancewarsa a wajen bikin bude sabon ofishin jakancin Amurka a birnin Kudus.

Sai dai kuma, tuni jakadan Najeriya dake Tel Aviv ya magantu, inda ya bayyana cewar sam shi bai halarci bikin da aka yi a birnin Kudus mai tsarki  ba.

 

LEAVE A REPLY