Tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan

Tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan yace, abinda ka dai zai sanya shi yin bacci da minshari, shi ne, dawowa da jam’iyyar PDP nasararta a babban zaben 2019 dake tafe nan gaba kadan.

Goodluck Jonathan, ya kuma dauki alhakin faduwar da jam’iyyar PDP ta yi a zaben da ya gabata na 2015, abinda ya kawo karshen mulkin PDP na tsawon shekaru 16 tana jan zarenta.

Yanzu abinda yake gabana, shi ne, naga nayi duk abinda zan iya wajen ganin jam’iyyarmu ta PDP ta samu nasarar dawowa kan karagar mulki a 2019, a dan haka babu ni babu yin dogon bacci, har sai na tabbatar PDP ta sake darewa kujerar Shugabancin Najeriya.

Tsohon Shugaban yana magana ne, a lokacin da tawagar me neman tsayawa PDP takarar Shubancinta Bode George suka kai masa ziyarar neman goyon baya a gidansa dake kauyensu na Otuoke a jihar Bayelsa.

“Ko na yadda ko ban yadda ba, dole na ne, na dauki alhakin faduwar PDP zaben 2015, domin nine na janyowa jam’iyyar wannan wawar asarar da ta yi ta Shugabancin Najeriya.” Haka aka jiyo Mista Jonathan yana fada yayin da ya karbi wannan tawaga.

“Babban abinda na sanya a gaba yanzu, shi ne, na tabbata munyi duk abinda zamu iya yi gwargwadon iko, wajen ganin PDP ta samu nasara a zaben Shugaban kasa dake tafe a shekarar 2019, wannan shi ne kadai abinda zai sanya nayi barci da saleba”

Tsohon Shugaban yace, yana nan yana aiki tukuru tare da dukkan masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar wajen ganin munyi dukkan wasu shirye shirye da zasu bamu dama ta sake dawowa  kan mulki.

Sannan kuma, tsohon shugaban yayi alkawarin ba za’a sake maimaita irin kurakuran da aka yi a baya ba, wadan da suka janyowa da jam’iyyar matsalar da ta kasa iya cin zaben Shugaban kasa a 2015.

A nasa jawabin, mai neman tsayawa karar Shugabancin jam’iyyar PDP, Bode George, ya yiwa Goodluck Jonathan fatan alheri a bisa cika shekaru 60 da yayi da haihuwa a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Sannan kuma, ya bukaci tsohon Shugaban ya zage dantse wajen ganin samun Nasarar jam’iyyar ta PDP tare da tabbatar da cewar Jam’iyyar ta dinke duk wata baraka kafin gudanar da babban taron jam’iyyar da za’a zabi sabon Shugaba a ranar 9 ga watan gobe.

LEAVE A REPLY