Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, a karon farko ya bayyanawa duniya cewar, ya fara shiga harkokin kasuwanci ne a shekarar 1971, a lokacin da ake aikin kwastan a jihar Legas, yana aiki kan iyakar Najeriya da ake kira Idi-Iroko.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne, ranar Alhamis a birnin Legas, yayin wani taron karrama shi, a matsayin mutmin da ya cimma kudurori masu yawa a rayuwarsa ta fuskar samar da aikin yi. Wanda kungiyar matasan Afurka masu rajin koyawa matasa sana’o’i ta bashi.

“Na zo birnin Legos ne a ranar 29 ga watan Yunin 1969, bayan na kammala samun horo na shekara biyu a matsayin jami’i a hukumar shige da fice ta kasa, daga nan aka turani zuwa kan iyakar Najeriya da ake kira Idi-Iroko. A wancan lokacin babu babbar hanyar nan ta cikin garin Legas da aka fi sani da Hanyar-Badagry. Bayan haka kuma, hanaya daya tilo da zata sadar da kai zuwa kasashen yammacin Afurka ita ce, hanyar kan iyaka ta Idi-Iroko, a lokacin ana kiranta da iyakar Dahomey, wadda a yanzu aka fi sani da Jamhiriyar Benin”

“A lokacin da na isa kan iyakar Idi-Iroko, a lokacin ko ayren fari ban yi ba. Sai na lura a wannan lokacin kasuwancin da yafi garawa shi ne, na harkar Sufuri da ‘yan gada gada suke yi, a wancan lokaacin Akori-kura ce take diban mutane daga Ajase ta kai su zuwa cikin garin Legas da safe, sannan da yammaci ta kuma kwaso su zuwa Ajase ko Foto-Nobo”

“Ganin haka yasa na tambayi kaina, ta yaya zan iya yin amfani da dama ta, domin nima na tsunduma cikin harkar sufuri da ‘yan gada gada suke yi. Kawai na yanke shawarar zuwa kamfanin SCOA, wanda a wannan lokacin shi ne babban kamfanin da yake samarda motoci a Najeriya, na samu jami’an kamfanin na sanya hannu akan kwantaragin karbar hayar motoci guda hudu da aka fi sani da Haya-faces, daga nan na samu ‘yan gada gada mutum hudu na hannata musu motocin nan, domin su dinga sufuri da su suna kawo balas, ni kuma a duk karshen wata, zan je kamfanin SCOA na basu abinda muka yi yarjejeniya akan zan dinga kawowa”

“Ba nida aure alokacin, dan haka, albashina, yana nan ko taba shi bana yi, bayan kuma gashi ina samun duk abinda zan batar a kudaden da nake karba na balas daga ‘yan gada gada da na baiwa hayar motocin da na dauko. A ko da yaushe idan kana sn samun nasara a duk wani aiki da ka fara, dole ka dage kayi aiki tukuru dominsa, da haka ne ake cin ribar duk abinda aka sanya a gaba”

A yayin wannan taro,Atiku Abubakar yayi bayanai masu ratsa zukata, inda yace, a baya tun kusan shekarun 1960,lokacin da tsarin karatun boko yake da daraja,ana baiwa dalibai horon yadda zasu dogara da kansu,idan basa son yin aikin Gwamnati, dan rike kansu da iyalansu.

“A tsarin karatun baya tun zamanin jamhuriya ta farko, idan dalibi ya gama Elimantare, yana da zabin ko dai ya tafi jami’ah don cigaba da karatunsa, ko kuma ya tafi makarantar kimiyya da aka fi sani da Technikal domin koyon wata sana’a da mutum yake son kwarewa akanta. A wancan lokacin babu wani dalibi da zaka ga yana gararamba da suna korarren dalibi, idan kwai mara fahimta da ba zai iya karatu ba, sai a tura shi makarantar koyon sana’a, ya zabi wadda yake so, kuma a bashi duk abinda yake bukata domin fara sana’ar dan dogaro da kansa”

“ABin takaici ne yadda Najeriya ta gujewa wancan tsarin, ta kama wani abu daban da ba zai taimaki dalibai da suke kammala karatu a yanzu ba, ta yadda duk wanda ya gama jam’ah yanzu kawai ya nade hannu yana neman aiki, alhali kuma aikin babu shi”

LEAVE A REPLY