A ranar Talata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, tun bayan da ta kama aiki a shekarar 2015, Gwamnatinsa ta ci nasarar dawo da makudan kudaden da aka sacewa Najeriya kafin zamansa Shugaban kasa.

Ya bayyana cewar yaki da cin hanci da rashawa a wannan zamanin ba abu bane mai sauki, sai jajirtaccen gaske ne zai iya wannan aiki, domin kana yakar cin hanci shima yana yakar ka.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya musanta zargin da ake yiwa Gwamnatinsa na nuna son kai wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ake zarginsa da kauda kai ga wadan da suke cikin jam’iyyarsa, yayin da ake kame ‘yan adawa kadai.

Shugaban ya bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da sabon ginin sakatariyar hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta EFCC dake da mazaunin a tsakiyar babban birnin tarayya Abuja.

 

 

LEAVE A REPLY