Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Tsohon hadimi ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, Mista Reno Omokri ya bayyana wasu muhimman abubuwa guda bakwai a suke da alaka da Gwamnati wanda Shugaba Buhari bai san da su ba.

Mista Omokri ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter,inda ya wallafa sunayen abubuwan da yace bai kamata ace Shugaba Buhari yana Shugaban tarayyar najeriya amma bai san da su ba, karkashin ikonsa.

Ya zayyana abubuwan kamar haka:

1- Shugaba Buhari bai san cewar Sifeton ‘yan Sanda ya bijirewa umarninsa ba.

2- Shugaba Buhari bai san cewar kasar Ghana tafi Najeriya karancin cin hanci ba.

3- Shugaba Buhari bai san cewar, an dade da dena ambaton kasar Jamus ta gabas ba.

4-Shugaba Buhari bai san sunan mataimakinsa ba, dan ya taba kiransa da Osibande.

5- Shugaba Buhari bai san cewar an yiwa kasafin kudi cushen abubuwan da bai shi ya sanya su ciki ba.

6- Shugaba Buhari bai san cewar, Abdulrasheed maina yana cigaba da aiki ba.

7- Shugaba buhari bai san cewar mai dakinsa bata cikin ‘Other room’ ba.

LEAVE A REPLY