Ministan Sufiri Rotimi Amaechi

Ministan harkokin sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi, yayi kira ga abokan aikinsa Ministoci da su mayar da hankali akan abubuwan da zciyar da Najeriya gaba, su daina dora laifin gazawarsu akan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Amaechi, yace yanzu ne lokacin da ya dace wannan Gwamnatin tamu ta mayar da hankali wajen cikawa mutane alkawuran da suka dauka musu a lokacin yakin neman zabe, ba kullum ayi ta dora laifin matsalolin da muka samar a kan tsohon Shugaban kasa ba.

“Na gamsu da masu ra’ayin cewar, mu daina dora laifin gazawarmu akan Gwamnatin da ta shude, mu muyi abin da zamu iya, wanda zamu iya nunawa al’umma dan su san cewar muma zamu iya, amma kullum muyi ta dorwa Gwamnatin Jonathan laifi ba shi  ne mafita ba”

“Jaridar The Nation ce ta ruwaito Mista Amaechi yana fadin hakan a ofishinsa lokacin da yake ganawa da wasu mutane a kebe, inda yaceyana takaicin yadda kullum ake dora laifin gazawar Gwamnatinsu akan Jonathan, alhali suna da damar da zasu iya gyara kura kuran Jonathan din da suke ta zargi”.

LEAVE A REPLY