Taron majalisar zartarwa ta Shugaban kasa na wannan makon, ya samu halartar ministoci 18 kacal a cikin ministoci 36 da ake da su a cikin majalisar zartarwa wadda Shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta.

A wannan makon, mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo ne ya jagorancin zaman majalisar.

Haka kuma, DAILY NIGERIAN ta habarto cewar, da alamar kasancewar Shugaba Buhari baya gida Najeriya ya sanya ministocin kin halartar zaman majalisar na wannan makon da mataimakin Shugaban kasa ya jagoranta.

Bayan dai da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a shekarar 2019, ya sa kafa ya bar Najeriya zuwa kasar Burtaniya domin yin hutun shekara.

Bayan haka kuma, rahotanni sun tabbatar da cewar Shugaban zai halarci taron kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka da za’a yi a birnin Landan.

Ministocin da suka samu damar halartar wannan zaman na wannan makon sun hada da Alhaji Lai Mohammed (Yada labarai), Abdulrahman Danbazzau (harkokin cikin gida), Chris Ngige (Kwadago), Adamu Adamu (ilimi), Adebayo Shittu (Sadarwa), Usani Usani (Neja Delta), Ogbonnaya Onu (Kimiyya da fasaha) and Rotimi Amaechi (sufuri).

Sauran su ne kananan ministoci da suka kunshi Zainab Ahmed (kasafi da tsare tsare), Steven Ocheni (kwadago), Anthony Onwuka (limi), and Heneiken Lokpobiri (Aikin gona).

Ragowar su ne Omole Daramola (Neja Dalta), Osagie Ehinare (lafiya) Hadi Sirika (harkokin jiragen sama), and Mustapha Baba Shauri (lantarki).

LEAVE A REPLY