A kalla Hausawa da Fulani 25 ne aka tabbatar sun mutu yayin da Masallatai guda biyu ke ci da wuta ganga ganga a jihar Binuwai, biyo bayan kashe wasu Kiristoci 17 da aka yi a wata Coci ranar Talata.

A cewar wani rahoto da BBC ta yi, matasan dauke da muggan makamai, sun tare hanyoyi inda suka dinga neman Hausawa ko Fulani su kashe ko duk wani Musulmi matafiya ko ‘yan gari.

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah wa ikamatus Sunnah na jihar, Sheikh Shuaibu, ya shaidawa BBC cewar shi da kansa ya kirga gawarwakin mutum 27 Musulmi wadan da maharan suka kashe a asibitin koyarwa na jihar.

Yace an kashe Musulmi da dama a yayin da Masallatai guda biyu ke ci da wuta.

Sai dai kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai har yanzu bata ce komai ba akan wannan batu.

Wasu mutane da ake kyautata zaton Fulani ne makiyaya, da sanyin safiyar Talata sun tasamma Cocin St. Ignatius Catholic dake Ukpor-Mbolom, dake yankin karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar Binuwa,inda suka kashe Fastoci guda biyu tare da kashe masu ibada guda 17 a cocin.

Harin da aka kai cocinya zo ne kwanaki hudu bayan da aka kashe wasu mutum 10, da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne dake yankinkaramar hukumar Goma suka kashe su.

LEAVE A REPLY