Tsohon Shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewar manyan Shugabannin Bankuna a Najeriya na matukar taimakawa ayyukan zambar kudade da kuma cin hanci da rashawa. Nuhu Ribadu yana bayyana haka ne a Abuja, yayi da yake gabatar da kasida wajen bikin kaddamar da wani littafi.

“Tsarin gudanarwar aikin banki a Najeriya, ya taimaka wajen baiwa miyagun mutane damar su saci kudade san ransu ba tare da an iya bin sawunsu cikin sauki ba, su manyan jam’an bankuna ake hada baki da su da miyagun mutane domin batar da sawun hanyoyin da za’a iya bi domin gano yadda kudade suke batan dabo”

Akwai muhimman dokoki da suka shafi mu’amalar kudade a Najeriya, amma sam ba’a cika aiki da su ko kokarin bibiyarsu ba yayin da za’a yi mu’amalar kudade, manyan ma’aikatan bankuna sun sani sarai da wadannan dokoki, amma sai suyi shakulatun bangaro da su, su yi gaban kansu wajen taimakawa barayi da miyagun mutane, matukar an cimma yarjejeniyar abinda zasu samu.

Mallam Nuhu Ribadu yace, matukar ana son cin nasara wajen yakar zarmiya da almundahana da kuma zambar kudade dole sai manyan Shugabannin bankuna sun ji tsoron Allah, kuma hukuma dole ta yi aiki da su wajen gano mafakar kudaden sata. A sabida haka, Nuhu Ribadu ya shawarci bankuna da su bayyanawa gwamnati duk wani irin garari da ya shafi harkar kudi a najeriya domin samun bakin zaren cikin sauki.

Ya kara da cewar, dole su manyan jami’an bankuna su hada kai tare da dukkan hukumomin da suke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati wajen bayar da bayanai domin samun nasarar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Bayan haka, Shugaban taron, kuma Gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefele, wanda ya sayi littafan domin amfanin Bankuna da jami’o’i, yace hanyoyin da kudade suke zurarewa zuwa hannun miyagun mutane, suna bukatar yin cikakken nazari sosai akansu, domin ta haka ne kadai za’a iya cin nasarar yakar zarmiya da almundahana.

Da yake nasa jawabin, mawallafin littafin Abdullahi Shehu, yace,musabbin rubuta wannan littafin nasa mai suna “Improving Anti-Money Laundaring  Compliance: Self-protectingTheory and Money Laundering Reporting Officers”ya bayyana cewar littafin zai tamakawa mutane mutane wajen samun nutsuwa da minci dangane da harkokin da suka shafi kudi masu sarkakiyar gaske.

 

LEAVE A REPLY