Manoman Shinkafa a yankin karamar hukumar Kura dake jihar Kano, a ranar litinin sun yi fatali da shirin Gwamnatin tarayya na basu tallafin noman shinkafa.

Shirin dai ya kunshi rarrabawa manoman shinkafar kayayyakin amfanin gona da suka shafi noman shinkafa, karkashin kungiyar manoman shinkafa ta kasa tare da hadin guiwar Babban bankin Najeriya CBN da kuma bankin manoma na kasa BOA.

Manoman karkashin jagorancin Shugaban kungiyar a yankin karamar hukumar Kura dake jihar Kano, Ado Sarkin-Noma sun yi fatali da shin, jim kadan bayan an kaddamarda shirin rarrabawa manoman shinkafar kayan tallafin daga manajan daraktan bankin manoma na BOA, Kabiru Adamu.

Da yale zantawa da manema labarai a yayin gabatar da shirin tallafin, Sarkin Kano ya bayyana cewar, shirin bayar da tallafin wanda ya kunshi rarraba buhunhunan irin shinkafa da kuma dukkan abubuwan da ake bukata yayin noman shinkafa.

Ya kara da cewar, tun kafin kaddamar da shirin rabon kayan tallafin, sai da suka bukaci kungiyar manoman da su duba dukkan abinda ya dace su yi kafin fara shirin rabon kayan tallafin, amma basu yi komai ba, sai daga baya.

“Muna tsammanin cewar za’a bayar da kayan tallafin ne a bisa tsarin Gwamntin tarayya tare da bayar da tallfin kayan da za’a bayar, domin taimakawa manoman”

“Amma daga bisani sai muka ga cewar abinda zamu bayar ya ninka sau biyu na ainihin abinda aka bamu. Mun shiga kasuwanni mun tambayi farashin kayayyakin abubuwan da za’a raba mana,amma sai muka ga na Gwamnati za’a bamu akan Naira 210,000 sabanin Naira 100,000 da muka gani a Kasuwa”

“Da farko an yi mana romon baka ne kan wannan tallafi, inda aka shaida mana abinda za’a bamu ba zai wuce Naira 60,000 ba domin Gwamnati ta sanya tallafinta cikin abinda ya kamata a bamu, amma sai muka ga sabanin abinda aka gaya mana”

“Ba zamu karbi komai ba daga cikin kayan da suke rabawa ba, har sai sun warware abinda suka kulla” A cewar Sarkin-Noma.

 

LEAVE A REPLY