Aisha Buhari
Kwamitin hadinguiwa na majalisar dinkin duniya mai aiki kan cututtukan  HIV da AIDS, ya nada matar Shugaban kasa, Aisha Buhari a matsayin jakadiya ta musamman mai lura da UNIAD, wani reshe na kungiyar da yake lura da yaduwar cutar kanjamau daga mahaifiya zuwa jaririnta, domin rage kaifin yaduwar hakan a Najeriya.
Jami’i mai lura da sashin sadarwa da kasashen duniya, Charles-Martin Jjuuko, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya bayar a ranar Asabar a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar jami’in, daraktan majalisar zartarwa karkashin babban zauren majalisar dinkin duniya, Michel Sidibe, shi ne zai gabatar da takardar nadin Hajiya Aisha Buhari a wannan matsayi a ranar Litinin 19 ga watan Maris a Abuja.
Yace, wannan nadi da aka yiwa matar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya biyo bayan irin kokarinta da kuma hazakarta wajen wayarda kan mata da yara kananan a Najeriya.
Mista Jjuuko, ya kara bayyana cewar, Aaisha Buhari zata taka rawa ne wajen kara alakanta mata da yara da harkokin da suka shafi lafiya, da kuma tabbatarda cewar mata masu juna biyu suna zuwa ana yi musu gwajin cutar kanjamau.

 

NAN

LEAVE A REPLY