Daga Hassan Y.A. Malik

Majalisar dinkin duniya a jiya Alhamis ta shawarci hukumomin tsaro a Nijeriya da su yi kokarin daukar matakan kare afkuwar hare-haeren da ka iya jawo rasa rayuka da dukiyoyin al’umma da zarar sun samu rahoton sirri kan faruwar hare-haren.

Madam Sewuese Torkuma, wacce ita ce mashawarciya ga majalisar dinkin duniya kan al’amuran jinsi ce ta bayyana hakan a garin Jos, a  yayin da ta kai wata ziyarar karfafa gwiwa ga rundunar ‘Operation Rainbow’, rundunar da jihar Filato ta kafa don yaki da hare-hare a jihar.

“Bai kamata a ce jami’an tsaro sai sun jira an kai hari akan al’umma ba kafin su fara fafutukar binciko wadanda suka aikata harin.

“Ya zama dole ku zama cikin shiri a kowane lokaci don kare faruwar hare-haren da ka iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi tare kuma da sanaya mata da yara su rasa matsuguni,” Ta ce.

Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su bawa mata dama su kai manya matsayi a harkar tsaron Nijeriya ta yadda za su bada muhimmiyar gudunmwa wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.

Madam Torkuma ta kai wannan ziyara ne da nufin isar da sakon majalisar dinki duniya ga rundunar ‘Operation Rainbow’ a kokarinta na kawo karshen nuna bambamci tsakanin jinsi musamman a harkokin zartarwa.

LEAVE A REPLY