Majalisar dattawa a ranar Laraba ta bayyana cewar zata iya kin amincewa da kasafin kudin ma’aikatun Gwamnati, idan har ska gaza mika bayanan yadda aka kashe kudaden kasafin shekarar da ta gabata ga babban mai binciken kudi na kasa.

Majalisarta yanke hukuncin hakan ne, bayan da ta amince da rahoton kula da kashe kudaden al’umma na majalisar, wanda Shugaban kwamitin Matthew Uroghide ya gabatar a gaban babban zauren majalisar.

Rahoton ya nuna cewar kashi 85 na hukumomin Gwamnati ciki har da Bankin Manoma BOA da hukumar yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, duk basa bayar da bayanan yadda suka kashe kudaden hukumominsu tun da aka kafa su.

Majalisar ta bayyana cewar, dole ne hukumomin su aika da bayanan yadda suka kashe kudaden ma’aikatunsu na shekara biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasarnan ya tanadar a sashi na 85.

A cewar Mista Uroghide, a cikin hukumomin Gwamnati guda 447, guda 40 ne kacal suka iya bayar  da bayanan yadda suke kashe kudadensu ga ofishin mai binciken kudi na kasa.

Ya cigaba da cewar, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewar, dole ne dukkan ma’aikatu da hukumomin Gwamnati su dinga baiwa babban mai binciken kudi na kasa bayanan yadda suke kashe kudaden ma’aikatunsu, sannan shi kuma ya aikawa majalisun dokoki na tarayya.

Dan majalisar ya kara da cewar, dole ne dukkan hukumomi da ma’aikatun Gwamnati su tabbatar asusun ajiyarsu, ana yi masa bibiya ta hanyar sanin abinda ya shiga da kuma yadda aka fitar da shi daga ofishin mai binciken kudi na kasa.

Yaa ce: “Hukumar EFCC ana da ra’ayin duk lokacin da suka zo domin kare kasafin hukumar, zasu bayar da bayanan yadda suka kashe kudaden shekarar da ta gabata, amma kuma dokokin da suka kafa hukumar sun tanadi cewar dole ne hukumar ta mika bayanan yadda ta kashe kudadenta watanni shida na shekarar kasafin kudi”

A lokacin da yake maida jawabi kan wannan batu, Shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya jininawa wannan cigaba da aka samu, yace matukar ba za’a abi abinda wannan kwamiti yace ba, to tamkar ana cigaba da daurewa cin hanci gindine.

Ya cigaba da cewa, “Abin mamaki ne kwarai ace acikin hukumomin Gwamnati 447 guda 40 ne kadai suke iya bayar da bayanan yadda suke kashe kudadensu. A lokacin da kuma irin wadannan hukumomi suke balokokon cewar majalisa bata abinda ya dace kan yakar cin hanci da rashawa”

“Lallai akwai gagarumar matsala a kasarnan, idan har za’a ce ma’aikatu da hukumomin Gwamnati 447 basa iya kare kudaden da suke kashewa duk shekara”

“A sabida haka yanzu mun dauki mataki,idan har sauran hukumomi da ma’aikatun Gwamnati sun yi abinda ya dace kamar yadda wadannan guda 40 suka yi na bayar da bayanan yadda suka kashe kudadensu na shekara biyu, to sannan zamu amince da kasafin kudinsu”

“Saboda haka, mu tuna cewar, a lokacin da muke tattaunawa kan batun kasafin kudi na shekarar 208, wannan kwamiti da suke gabatar da wannan rahoto nasu, muna fatan zaku dinga bamu bayanan dukkan ma’aikatu da hukumomin da suka mika bayanan ga ofishin babban mai binciken kudi na tarayya”

“Daga zarar mun samu zarafi, zamu yi magana da Sakataren Gwamnatin tarayya SGF domin tabbatar da cewar dukkan hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin tarayya suna mika bayanan yadda suka kashe kudadensu” A cewar Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

NAN

LEAVE A REPLY