Shugaban majalisar Dattijai Sanata Abubakar Bukola Saraki

Kwamitin majalisar dattawa mai lura da man fetur da dangoginsa, ya zargi kamfanin mai na ƙasa NNPC da masu kasuwanci da dillancin mai a Najeriya da laifin karancinsa da ake fama da shi a ko ina a wannan lokaci.

Shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Marafa ne ya bayyana hakan ranar litinin a Gusau a yayin da yakai ziyarar gani da ido wasu gidajen mai a Gusau domin ganin yadda matsalar take addabar ‘yan Najeriya.

Sanata Marafa wanda yake tare da daya daga cikin memban kwamitin Abdullahi Danbaba, ya bayyana cewar, wannan zagaye da suke yi domin ganin halin da al’umma suke ciki na wahalar mai, yana daya daga cikin ayyukan kwamitinsa, wanda Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya dora masa.

“Na baiwa dukkan ‘yan kwamiti na umarni da su koma mazabunsu, domin su duba mana irin yanayin yadda matsalar mai take a yankunansu, domin samun saukin hanyoyin da zamu bi don ganin an kawo arshen wannan wahalar mai da ‘yan Najeriya suke sha”

“Mun ziyarci babban defo na NNPC dake Gusau domin gani tare da duba irin adadin man da ake turo musu domin rarrabawa, amma abin mamaki adadiin da muka ganin ba shi da yawa kwarai da gaske, abinda yake sa dole a sha wahalar samunsa”

“Zamu shirya rahoto na musamman da zamu gabatarwa da zauren majalisar dattawa. Gaskiya abu ne marar dadi irin yadda muka ga ‘yan Najeriya na cikin tsananin a dalilin karancin man nan da ake fama da shi a kasarnan”

“A gaskiya mun diga ayar tambaya akan kamfaninmai na kasa NNPC, domin mun jiyo shugaban kamfanin Dr. Maikanti Kachalla Baru yana cewar sun ninka yawan adadin man da suke turawa defo defo din da suke da shi a fadin Najeriya, amma abinda muka gani ya saba da abinda ya fada”

“Wani abin karin takaici shi ne, duk da karancin man da ake fama da shi maimakon a sayarwa da jama’a shi, sai a canza masa akala inda ake sayarwa da ‘yan bumburutu ta hanyar bakar kasuwa, wanda wannan abin takaici ne kwarai da gaske”

“A duk zagayen gidajen man da muka yi, guda biyu ne kadai muka tarar suna bin dokar da aka bayar kan rarrabawa tare da sayarwa da jama’a man da suke da shi, a cewarsa, kazamar cuwa cuwa tayi muni a harkar” A cewar Sanata Marafa.

Sannan kuma Sanata Marafa ya jinjinawaofishin shiyya na DPR wajen dogewarsu kan yadda suke karba tare da amsa korafe korafen jama’a akan karancin man da ake fama da shi. Sannan kuma, Sanatan ya bukaci DPR da su karbe lasisin duk wani gidan mai da aka samu suna sayarwa sama da naira 145 akan kowace lita.

NAN

 

 

LEAVE A REPLY