Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

Majalisar dattawa a ranar Alhamis, ta dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege, mai nuna tsananin goyon baya ga Shugaba Buhari, saboda ya nuna adawa da sake fasalin jadawalin zaben 2019 da majalisar ke shirin tabbatarwa.

Idan za’a iya tunawa, Sanata Omo-Agege a watan fabrairu, ya zargi abokan aikinsa da yiwa Shugaba Buhari bita da kulli, ta hanyar biyewa sashi na 25 na kundin dokokin zabe da ya bayar da dama domin sauya fasalin zabubbuka.

A lokacin da aka gabatar da batun gaban zauren majalisar dattawa, Shugaban majalisar Bukola Saraki, ya nemi kwamitin dake kula da da’a da su gudanar da bincike kan zargin da Sanatan ya yiwa abokan aikinsa.

A lokacin da yake gabatar da rahotonsa a ranar Alhamis, Shugaban kwamitin, Sam Anyanwu ya bayyana dakatar da Sanatan har na tsawon kwanaki 180.

Ya bayyana cewar, daukar wannan hukuncin ya zama dole saboda yadda Sanatan ya nuna rashinda’a ta hanyar kai batun kotu, bayan kuma majalisar dattawa ta mika lamarin gaban kwamitin da’a.

Sai dai kuma, majalisar ta mayar da kwanakin dakatarwar zuwa kwana 90 bayan da Shugaban majalisar Bukola Saraki ya nemawa Sanatan rangwame.

A lokacin da tattaunawa ta yi zafi a zauren majalisar, DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewar Sanata Omo-Agege yana mai cewar “Wasu daga cikinku da suke bibiyar abubuwan da suke faruwa a zauren majalisar wakilai, mambobi 36 ne kacal da suke zauren majalisar basu kai ace an zartar da wannan doka ta sake sauya fasalin zabe ba”

“Matsayar da muka dauka kan wannan batu, ita ce, mambobi 36 ba zasu iya yanke hukuncin abinda ya shafi mutane 360 da suke zauren majalisar wakilai ba, wanda yanzu aka turo shi zuwa zauren majalisar dattawa mai wakilai mutum 109. Zai zama akwai rashin hikima ace majalisar dattawa ta yi aiki da abinda ‘yan tsiraru suka yanke”

“Muna da Sanatoci guda 59, wadan da suke adawa da wannan sashi na 25 na kundin dokar zabe. Idan har aka ce wannan matsala ta cigaba har zuwa yau, Sanatoci 59 sun isa su zabi a cire wannan sashi na 25 na kundin dokokin zabe”

“Ba zai yu muyi doka saboda mutum guda ba. Abin da yake a kasa shi ne, an fake da wannan sashi na 25 ne kawai domin Shugaban kasa”

Wannan hukunci da majalisar dattawa ta dauka yana zuwa ne, sati guda bayan Dino Melaye ya ja hankalin majalisar dangane da kalaman da Sanata Omi-Agege ya yi kan takwarorinsa na majalisar.

LEAVE A REPLY