Daga Hassan Y.A. Malik

Bayan kin amsa gayyatar majalisar dattawa da sufeto janar na ‘yan sanda Nijeriya, Ibrahim Kpotun Ibrahim ya yi a karo na 3, majalisar ta bayyana rashin jin dadinta inda a nan take ta shiga wani zama na sirri don yake hukuncin ladabtarwa akan sufeton ‘yan sandan.

Zaman sirrin ‘yan majalisar dattawan da aka fara shi da karfe 12:24 na ranar yau Laraba ya dauki  tsawon minti 50 ana yi, inda daga karshe bayan an fito daga zaman ne shugaban majalisar dattawan, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bayyana hukuncin da majalisar ta yanke akan sufeton ‘yan sandan.

Majalisar a zaman nata ta bayyana halayyan sufeton ‘yan sandan a matsayin izgili ga sashen dokar kasar nan wanda hakan ya tabbatar da shi a matsayin ‘Makiyin Dimokuradiyya’, inda hakan ke nufin sufeton ‘yan sandan bai cancanci rike wani mukamin gwamnati a ciki ko wajen Nijeriya ba.

In ba a manta ba dai, majalisar dattawan ta fara gayyatar sufeton ‘yan sandan ne a ranar 25 ga watan Afrilu, inda sai a ranar da ya kamata ya bayyana a gabansu  ne ya aiko musu da sakon cewa ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari rakiya zuwa Bauchi.

Majalisar ta sake saka ranar 2 ga watan Mayu a matsayin ranar da sufeton ‘yan sanda zai hallaci zauren majalisar, amma sai majalisa ta yi ta tsumayinsa babu shi babu amonsa, sai daga baya suka samu labarin yana Kaduna.
Gayyatarsa da majalisar ta yi don ya bayyana a gabanta a yau shi ne na uku, amma sufeton na yin kunnen uwar shegu da bukatar majalisar.

LEAVE A REPLY