Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

Majalisar  dattawan Najeriya, a zamanta na yau, ta bayyana cewar, maganar da Sanata Shehu Sani yayi na cewar ko wanne sanata na karbar naira miliyan 13.5 duk wata a wata tattaunawa da yayi a makon da ya gabata, cewar maganarsa Sanatan na kan hanya.

A wata tattaunawa da Sanata mai wakiltar jihar kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa yayi da mujallar TheNews, ya bayyana cewar kowanne sanata yana karbar naira miliyan 45 duk wata uku a matsayin kudaden gudanar da ofis dinsu.

Wadannan kudade a cewar Sanata Shehu Sani, alawus ne da basa cikin albashin da ake biyan dan majalisar dattawa duk wata. A yayin da yake tattaunawa da mujallar ya bayyana cewar ana baiwa kowanne dan majalisar dattawa Naira 700,000 a matsayin albashi kowanne wata, yayin da suke karbar alawus din miliyan 13.5 duk wata.

Sai dai kakakin majalisar ta dattawa, Aliyu Abdullahi, ya are batun da cewar, wadannan kudade da ake baiwa ‘yan majalisar dattawa, babu wani  batu na boye boye ko kumbiya kumbiya a cikinsa, a cewarsa, wadannan kudade da ake baiwa ‘yan majalisar yana cikin kasafin kudin majalisar, wanda ake yin sa a bayyana.

A cewar Mista Abdullahi, kasafin kudin majalisar ya tanadi dukkan irin kudaden da za’a baiwa ‘yan majalisar dattawa, a cewarsa ba wani abu bane da aka yi a boye, domin a bainar jama’a aka gabatar da wannan kasafin kudi, ba kawai daki aka shiga aka rubuta aka mince da shi ba.

Acewarsa, babu wani abu sabo da Sanata Shehu Sani ya fadi game da irin kudaden da ‘yan majalisar ta dattawa suke karba.

Ya kara da cewar, dukkan masu rike da ofisoshin gwamnati musammanwadan da aka nada,ana basu kudaden gudanar da ofis dinsu, wannan kuma ba wani sabon abu bane da za’a tuhuma a cewar kakakin majalisar ta dattawa Aliyu Abdullahi.

 

LEAVE A REPLY