Abdulrasheed Maina

Ana samun karon baki tsakanin hukumar EFCC da majalisar dattawa kan matakin da ya kamata kan batun dawo da dakataccen ma’aikacin gwamnatin tarayyar nan Abdulrasheed maina. Tuni dai hukumar EFCC ta garkame gidan mainan dake Abuja, wanda darajar gidan takai dalai Amurka miliyan biyi ($2m).

A nata bangaren, bayan tattaunawa mai tsawo,majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki badakalar ko su waye ke da hannu wajen dawo da Abdulrasheed Maina bakin aikinsa. Aikin Kwamatin zai binciko tare da gano su waye ke da hannu akan maido shi bayan da aka kore shi daga aikin, har kuma aka samu anyi masa karin girma a yanzu.

Sanata Isa Hamma Misau daga jihar Bauchi ne ya kawo batun zauren majalisar dattawa, yana mai cewar batu ne na “gaggawa” da bai kamata majalisar tayi kasa a guiwa kansa ba, inda nan take ‘yan uwansa ‘yan majalisar sukai ammanar a tattauna batun a zauren majalisar.

Sanata Misau, ya kara da cewar, “Shugaban kasa ne kadai yake batun yaki da cin hanci da rashawa, amma duk na kewaye da shi sun ci sun tayar da kai da cin hanci da rashawa”.

Daga bisani kuma, Sanata Olusola Adeyeye daga jihar Osun, yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gurfanar da duk wanda aka samu da laifin kan badakalar dawo da maina gaban kuliya.

Shima da yake tofa nasa albarkacin bakin, Sanata Aidoko Ali, yace yaga baiken Antoni Janar kuma Ministan Shari’ah Abubakar Malami, yadda aka samu hannunsa dumu dumu kan wannan batu.

Yace, ya kamata shugaban kasa ya sani, Ministan Shariah yaci zarafin ofishinsa kan hannunsa da aka samu cikin wannan badakalar.

Sanatoci da dama ne dai suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu da ya dauki hankalin kusan galibin kafafen watsa labaran najeriya da ma na wasu kasashen ketare.

Hukumar EFCC dai na zargin Maina da barnatar da kudin fanshon ‘yan sanda da ya kai kusan Naira biliyan biyu.

Ko ya zata kaya kan wannan batarnaka? DAILY NIGERIAN HAUSA zata cigaba da bibiyar wannan batu, domin kawo muku yadda take wakana.

LEAVE A REPLY