Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a yau Alhamis ta bayyana inda da kuma yadda ta samo sandar majalisar dattawa da wasu tsageru suka kutsa kai har cikin zauren majalisar a jiya Laraba suka sace.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wasu tsageru da ake zargi Sanata Ovie Omo-Agege da majalisar ta dakatar ne ya turo su sun yi fadar majalisa tsinke a jiya Laraba kuma suka yi awon gaba da sandar majalisar.

Wadannan tsageru da adadinsu ya kai 15 sun shigo har zauren majalisar a lokacin majalisar na zamanta kuma suka wafce sandar majalisar suka yi tafiyarsu da ita.

Jami’an tsaro dai tuni suka cafke Sanata Omo-Agege, wanda shi kuma ya nisanta kansa daga sace sandar.

Sanarwar da mataimakin kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Aremu Adeniran ya fitar ta ce, ‘yan sanda sun samu gano sandar ne ta hanyar yin kofar ragio ga duk wata hanya da za ta fitar da mutum daga birnin tarayya Abuja, sannan kuma ‘yan sanda sun samu rahotannin tsaro daga wani daan kasa na gari da ya yi zargin inda aka ajiye sandar.

Tsananta bincike da ‘yan sanda suka yi a ciki da kan hanyoyin shiga da fita birnin tarayya manya da kanana, ya tilasta barayin sandar suka ajiye sandar a karkashin wata gadar sama kusa da kofar shiga birnin tarayya Abuja, inda wani dan kasa na gari ya ga sandar kuma ya sanar da ‘yan sanda.

Sai dai ‘yan sanda bisa umarnin Sufeta Janar na ‘yan sanda, Ibrahim K. Idris, sun shiga bincike kan yadda aka shigo majalisar aka kuma dauke sandar ta majalisa da kuma wadanda suka shirya wannan sata.

Hukumar ‘yan sandan Nijeriya na mika godiyarta ga kafatanin mazauna garin Abuja bisa hadin kan da suka basu a yayin da suke gabatar da cajen ababen hawa don gano sandar majalisar da aka sace a jiya, da kuma bayanan sirri da suka yi ta samu daga wajen ‘yan kasa na gari har zuwa lokacin da aka samu bayanin inda wadancan bata gari suka yasar da sandar.

Hukumar ta jaddada burinta na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin ‘yan Nijeriya tare da tabbatar da dimokuradiyya mai dorewa a fadin Nijeriya.

LEAVE A REPLY